An Gano Cutar Da Ke Sa Shugabannin Najeriya Sata

Wani masanin halayyar dan adam kuma likitan masu taɓin hankali Farfesa Ernst Josef Franzek ya bayyana cewa wani nau’in hauka ne ke sanya shuwagabannin ƙasar nan ɗabi’ar satar kuɗaɗen al’umma. Farfesa Franzek wanda ya kwashe shekaru 40 yana bincike a fannin hankali da kwalkwalr dan Adam, ya kasance baturen ƙasar Jamus. Da ya ke amsa akan dalilin da ya sa shugabannin ƙasar nan ke sata, sai ya ce “Attajirai a Najeriya suna samun kuɗi, amma ƙwaƙwalwarsu ta mutu, su kuma talakawan basa iya furta ra’ayinsu har ya yi tasiri.” Farfesan…

Karanta...

Dr. Omar Farouk Ya Zama Sabon Shugaban Masu Sarrafa Albarkatun Mai

Kungiyar masu sarrafa albarkatun mai na Africa (African petroleum producers ta bada sanarwar nadin Dr .Omar Farouk Ibrahim daga kasar Najeriya a matsayin sabon shugaban kungiyar. Dr Omar Farouk ya karbi ragamar jagorancin ne a hannun H.E Mahaman Laouan Gaya wanda wa’adin mulkin sa ya kare a yau. An cimma matsayar nadin Dr. Farouk ne bayan wani zama na musamman da masu ruwa da tsaki na kungiyar (APPO) da sauran ministoci sukayi yau a babban birnin tarayya Abuja. Dr Farouk ya nada kwarewa a harkan mai sosai inda ya rike…

Karanta...

Muna Da ‘Yanci A Daina Mana Katsalandan Daga Waje – Buhari

Kakakin Yada Labarai na Shugaba Muhammadu Buhari, ya gargadi Amurka, Ingila da Kungiyar Tarayyar Turai su daina shiga sha’anin Najeriya, musamman idan ana maganar zargin take hakkin dan Adam. Femi Adesina ne ya yi wannan gargadin jiya Laraba, yayin da ya ke maida martani ga wani rahoto da Turai, Ingila da Amurka suka fitar a kan Najeriya, wanda bai yi wa Gwamnatin Buhari dadi ba. Kasashen sun bayyana cewa Najeriya a sahun gaba na kasashen da suka yi kaurin suna wajen take hakkin jama’a. Adesina ya yi wannan bayani ne…

Karanta...

Kano: Sanusi Ya Kauce Haɗuwa Da Bayero

Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya juya tare da ‘yan rakiyarsa daga shiga harabar Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano, ana hasashen Sarkin ya ɗauki matakin hakan ne saboda halartar Sabbin Sarakuna daga Masarautun Bichi, Gaya da Rano, wajen bikin yaye dalibai na farko a Jami’ar. Wannan mataki da Sarkin ya ɗauka ya jefa jama’a da yawa cikin mamaki a waje taron. Saboda an ji kade-kaden motarsa da bushe bushen kakaki, amma sai ya juya ya bar filin taron. An samu ra’ayoyi mabanbanta akan matakin da Sarkin…

Karanta...

Bai Dace Masu Mulki Su Riƙa Bijirewa Umarnin Kotu Ba – Sarkin Musulmi

A Ranar Alhamis, 12 ga Watan Disamban 2019, Mai girma Sarkin Musulmi watau Sultan na kasar Sokoto, Alhaji Sa’ad Abubakar II, ya yi gargadi game da rashin bin hukuncin Alkalan kotu. Sarkin Musulmin ya nuna cewa sabawa umarnin kotu zai jawo rashin aiki da doka a kasar nan. Sa’ad Abubakar II ya yi wannan jawabi ne da ya ke magana a wajen wani taro a Garin Abuja. Hukumar NIREC ta addinan Najeriya ce ta gudanar da taron zangon karshe na wannan shekarar wanda ta yi a kan tasirin Malamai da…

Karanta...

Na Yi Tir Da Shigar Tsiraici Da Rahma Sadau Ta Yi – Musa Mai Sana’a

“Ba ki isa ki shigo Kano ki yi mana biki da Gwiwowi a waje ba, saboda Kano garin Musulunci ne”, sakon Musa Mai Sana’a ga Rahma Sadau. Musa Mai Sana’a kwantar da hankalinka, Rahama Sadau idan ta ga dama zatayi tsirara haihuwar uwarta ta shiga Kano tayi abinda ta ga dama babu abinda zai faru, mutanenta zasu iya daukar mata masu bata kariya daga ko’ina a sassan duniya, asalima tsarin dokar Kasa na Constitution da mulkin Demokaradiyyah na goyon bayan dabi’ar Rahama Sadau. Allah Madaukakin Sarki Ya fadawa Manzon tsira…

Karanta...

Za A Daina Shigo Da Tataccen Mai Daga Waje – Fadar Gwamnati

Gwamnatin tarayya ta sanya shekarar 2023 a matsayin lokacin da za ta daina shigo da man fetir wanda aka tace daga kasashen waje gaba daya, domin tana sa ran zuwa lokacin matatun man fetirin Najeriya sun mike tsaye. Gidan talabijin na Channels ta ruwaito shugaban hukumar man fetir ta Najeriya, Mele Kyari ne ya bayyana haka yayin da yake rattaba hannu kan yarjejeniyar tsarin samar da kananan matatun mai a Najeriya da zasu dinga samar da litan tataccen mai miliyan 20. Kasar Najeriya dai ta dogara ne da tataccen man…

Karanta...

Dattawan Daura Sun Koka Akan Yawan Korafin Aisha Buhari

Dattawan Birnin Daura Garin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari sun kalubalnci matarsa, Aisha, kan kalaman da ta yi a ranar Laraba inda ta soki Mamman Daura da hadimin shugaban kasar na musamman, Garba Shehu. A hirar da su kayi lokuta daban-daban da wakilin jaridar The Punch a yammacin ranar Laraba, Dangin shugaban kasar sun soki Aisha Buhari kan katsalandan kan abinda suka kira fallasawa duniya harkokin cikin gida. A cikin sanarwar da ta fitar a ranar Laraba, Aisha Buhari ta ce “Garba Shehu ne ya ce gwamnati za ta dakatar da…

Karanta...

Kaduna: ‘Yan Bindiga Na Cigaba Da Satar Mutane

Rahotannin da muka samu daga garin Juji na yankin ƙaramar hukumar Chikum dake jihar Kaduna na tabbatar da cewa wasu mutane da ake zargin masu garkuwa da mutane kimanin su 20 sun shiga garin na juji da misalin karfe daya na dare inda suka dinga harbi kan mai uwa da wabi. Sun shiga wani gida tare da yin awon gaba da wata mata mai suna Okeke da yaran ta biyu. Sun kutsa kai ne a daren jiya da misalin karfe dayan dare tare da yin harbin kan mai uwa da…

Karanta...

‘Yan Najeriya Na Yi Mana Kallon Azzalumai – Shugaban Majalisar Dattawa

Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya ce, ‘yan Najeriya na yi wa sanatoci kallon mutanen banza azzalumai saboda basu fahimtarsu. Shugaban majalisar dattijan ya sanar da hakan ne a ranar Talata yayin jaddada cewa majalisar dattijan zata yi duk abinda ya dace don habaka yarda tsakaninta da ‘yan Najeriya. Wannan ya biyo bayan bukatar da Sanata Ahmed Babba Kaita ya mika gaban majalisar ta sauya sunan babbar makaranta ta Daura zuwa sunan marigayi Sanata Mustapha Bukar, wanda ya rasu. A jawabinshi bayan karatun bukatar kashi na biyu, Lawan ya ce,…

Karanta...