Ba Maulidi Muka Je Fadar Shugaban Kasa Ba – Alaramma Suleiman

Sanannen mahaddaccin Al- Ƙur’ani na kungiyar Izala Alaramma Ahmad Suleiman, ya bayyana cewar gayyatar da Uwargidan Shugaban kasa A’isha Buhari ta yi wa Malamai zuwa fadar shugaban kasa, gayyata ne akan yi wa ƙasa addu’a da kuma cigaban ƙasa, amma ko kaɗan gayyatar ba ta da alaƙa da taron maulidi kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka rinƙa yayatawa. Alaramma Suleiman ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu ta wayar tarho dangane da ziyarar da malamai suka kai fadar shugaban kasa a yau. Babban Alaramman ya cigaba…

Karanta...

Izala Da Ɗariƙa Sun Halarci Taron Maulidi A Fadar Shugaban Kasa

Malaman Izala Da Na Darika Sun Halarci Taron Maulidin Manzo SAW Da Yi Wa Kasa Addu’a Da Aisha Buhari Ta Gudanar A Villa Uwargidan shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari ta gudanar da taron Maulidin Manzon Allah S.A.W tare da yi wa ƙasa addu’a. An gudanar da taron ne a safiyar yau Litinin 11 ga watan Nuwamba, 2019, a dakin taro na banquet Hall dake fadar gwamnatin tarayya Abuja.

Karanta...

Zargin Maɗigo: Kotu Ta Kori Ƙarar Da Amal Ta Kai Gabon

Babbar kotun tarayya mai lamba 2 dake Kano wadda mai Shari’a O, A, Oguata ya ke jagoranta, a shekaran jiya juma’a, ta kori karar da Amina Amal ta shigar a gaban ta in da take neman kotun ta bi mata hakkin ta a wajen Hadiza Gabon saboda bata mata suna da ta yi. Tun a watan Afrilun da ya gabata ne dai Amina Amal ta shigar da karar in da Amal take bukatar kotun da ta Sanya Hadiza Gabon ta yi Abu hudu wadanda suka hada da ta bata hakuri…

Karanta...

Zamfara: ‘Ya’yan APC Dubu 21 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP

Kimanin ‘yan jam’iyyar All Progressives Congress, APC, 21,000 sun sauya sheka zuwa babbar jam’iyyar da ke ci a jihar Zamfara, Peoples Democratic Party, PDP. Wadanda suka sauya shekan sun samu tarba daga gwamnan jihar, Bello Matawalle, da shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Alhaji Ibrahim Mallaha, a Gusau, babbar birnin jihar ranar Lahadi. Yawancin wadanda suka sauya shekarn ‘yan karamar hukumar Maradun ne, mahaifar gwamnan. A taron, gwamnan ya yabawa sabbin yan PDP kan daukan wannan mataki da zai ciyar da jihar gaba. Ya yi kira ga mazauna jihar Zamfara su…

Karanta...

Borno: Mayakan Boko Haram 16 Da Iyalansu Sun Mika Wuya

Wasu mutane 16 da suka tabbatar da cewa su mambobin kungiyar Boko Haram ne da takwararta ISWAP sun mika kansu ga rundunar sojin Najeriya a jihar Borno, kamar yadda jaridar Tribune ta rawaito. An alakanta mika wuyan mayakan da matsin lambar da suke fuskanta daga dakarun soji, wadanda ke cigaba da kaddamar da hare-hare a sansani da maboyar mambobin kungiyoyin ta’addanci da ke yankin arewa maso gaba. Shugaban sashen yada labarai na rundunar soji, Kanal Aminu Iliyasu, shine wanda ya sanar da hakan a cikin wani jawabai da ya fitar…

Karanta...

Kano: Sarki Sunusi Ya Bukaci A Hukunta Iyayen Da Aka Sace’Ya’yan Su

Mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi ya tofa albarkacin bakinsa a game da wasu kananan yara da aka sace daga jihar Kano inda aka tsere da su zuwa Garin Onitsha da ke jihar Anambra. Daily Nigerian ta ruwaito Sarkin ya na cewa ya kamata a daure Iyayen da su ka yi sake har aka sace ‘Ya ‘yansu. Muhammadu Sanusi II ya ce Iyayen sun kyale yaran ne su na gararamba. Sarkin na Birnin Kano ya yi wannan jawabi ne wajen wani taro da wata kungiya mai suna LESPADA ta shirya domin…

Karanta...

Buhari Ya Gana Da Limamin Cocin Canterbury A Fadar Lambeth Dake Birnin Landan

Shugaba Muhammadu Buhari ya kaiwa abokinsa, Archbishop na Canterbury, Rabaran Justin Welby, fadar Lambeth dake Landan ranar lahadi. Akwa Kyakkyawar alaƙa tsakanin shugaban da babban Limamin Cocin shekaru masu yawa, wanda jama’a ke ganin babu yadda za’a yi Buhari ya shiga ƙasar Ingila ba tare da sun gana da juna ba. A jinyar da shugaban ya yi a kwanakin baya a ƙasar ta Birtaniya, babban Limamin Cocin ya kasance yana yawaitar ziyarar Buhari akai-akai, alaka ce da jama’a ke ganin akwai yarda da amana a tsakanin su. Tafiyar shugaban kasar…

Karanta...