Ya Dace A Rage Yawan Sanatocin Najeriya – Okorocha

Dan majalisar dattawan Najeriya Sanata Rochas Okorocha ya yi kira a rage yawan ‘yan majalisar dokokin kasar da zummar kawo karshen kashe kudin gwamnati babu gaira babu dalili. Sanata Rochas, wanda tsohon gwamnan jihar Imo ne, ya bayyana wannan matsayi ne a zauren majalisar ranar Alhamis. Ya ce “tsarin mulkin Najeriya ya bukaci a samu Sanata uku daga kowacce jiha. Ina ganin hakan bata kudi ne. Don haka ya kamata a kowacce jiha a samu sanata guda daya. Mene ne amfanin sanatoci masu yawa? Mene ne amfanin ‘yan majalisar dokoki…

Karanta...

An Bada Belin Sawore

A yau Juma’a Babbar Kotun Tarayya ta bayar da belin Omoyele Sowore, a kan kudi naira milyan 100. Kotu ta ce sai masu karbar beli biyu sun ajiye naira milyan 50 kowanen su, sannan za a karbi belin sa. Sannan kuma za su kasance mazauna Abuja ne, kuma kada su fita daga Abuja. Haka nan kuma kotun ta ce idan Sowore ya samu kan sa, aka karbi belin sa, to kada ya kuskura ya shiga zugar wata zanga-zanga, ko wani taro mai kama da haka. A yau ne dai lauyan…

Karanta...

Ba Zamu Iya Ƙarin Albashi Ba Sai Mun Rage Ma’aikata- Gwamnatin Tarayya

Ministan Kwadago da Inganta Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Chris Ngige, ya bayyana cewa babu yadda za a yi Gwamnatin Tarayya ta iya dorewa da biyan albashi kamar yadda Kungiyar Kwadago ke bukata, har sai an rage ma’aikata tukunna. Ngige ya ce gwamnatin tarayya na bukatar karin kudi zunzurutu har naira bilyan 580 domin biyan karin albashi. Tun dai cikin watan Afrilu ne Shugaba Muhammadu Buhari ya sa wa dokar karin albashi hannu, amma ga shi wata bakwai kenan bayan da Majalisar Tarayya ta mika masa kudirin, ba a fara biya ba.…

Karanta...

Ƙarin Kuɗin Haraji: Ba Na Goyon Bayan Gwamnati Ko Kaɗan – Ndume

Dan majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Muhammad Ali Ndume ya shawarci gwamnatin Najeriyar game da yunkurinta na kara harajin kaya domin samun karin kudi yana mai cewa a maimakon haka, kamata ya yi gwamnatin ta bijiro da tsarin karbar haraji daga masu amfani da waya. Sanata Ndume ya ce idan har gwamnati ta aiwatar da Karin harajin kaya, toh kuwa talaka ne zai shiga halin ni-‘ya-su ta yadda farashin komai a kasuwa zai daga kama daga farashin mai da magani da mota da abinci. Sanatan mai wakiltar Borno ta kudu a…

Karanta...