Borno: Gwamna Zulum Ya Biya Wa Dalibai 24,323 Kudin Jarrabawar WAEC

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya amince da sakin naira million dari da hamsin da biyu da digo shida N152.6M na biyan kudin jarabawar dalibai 24,323 na daliban jahar Borno da suka rubuta jarabawar WAEC na bana May/June 2019. Mai magana da yawun Gwamnan Malam Isa Gusau shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a, a cewar sa, kamar yadda Gwamnatin jihar Borno ta saba na biyan kaso 45%, karamar hukuma kuma kaso 30%, da kuma iyayen yara su biya kaso 25% cikin…

Karanta...

Saudiyya Ta Dauki Bahaushe Yin Wa’azi A Masallacin Annabi

Kasar Saudiyya, ta zabi harshen Hausa cikin jerin harsunan duniya da za a rika yin amfani da su wajen gabatar da tunatarwa a cikin babban Masallacin Madina, ma’ana dai, babban Masallacin Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi. Hukumomin Saudiyyar sun zabi Dakta Magaji Falalu Zarewa, tare da aza masa wannan nauyi na rika gabatar da karatuttuka da kuma tunatarwa a cikin wannan Masallaci mai albarka da ke samun halartar dimbin baki da kasar Nijeriya Hausawa da kuma sauran al’umma daga kasashe daban-daban masu jin…

Karanta...

Kaduna: An Garkame Gidajen Man Fetur 53

Hukumar Kula da Saida Man Fetur ta Kasa, wato DPR, shiyyar Kaduna, ta kulle gidajen saida man fetur da gas har 56 a cikin jihar Kaduna. DPR ta bayyana cewa ta kulle gidajen man ne saboda sun ki bin ka’idojin da suka jibinci sayar da fetur a gas a fadin duniyar nan. Babban Jami’in DPR mai kula da Shiyyar Kaduna, Isa Tafida ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zagayen gani-da-ido a kan gidajen mai na watan Yuli a jihar Kaduna. Ya ce sun gudanar da samamen kulle…

Karanta...