An Damke Mawallafin Jaridar Sahara

Jami’an tsaro ‘yan sandan Farin Kaya wato DSS sun dira a gidan mawallafin jaridar Sahara Reporters da ke yada labaranta a Shafukan yanar gizo gizo, kuma dan takaran shugaban kasa a jam’iyar ACC, mai suna Omoyele Sowore a yau din nan Asabar. Ana kyautata zaton kama dan jaridar na da alaka da kiraye-kirayen da akaji yana yi kwanan nan na Neman a yi wa gwamnatin shugaban kasa Buhari juyin mulki duba da yadda tafiyar gwamnatin ta kasa gamsar da Jama’a, inji shi. Kafin a kamashi Omoyele Sowore, na shirin jagorantar…

Karanta...

Ko Kungiyar Kwallon Najeriya A Yanzu, Za Ta Kamanta Abin Da Na Baya Suka Yi?

A rana mai kama ta yau a shekarar 1996 tawagar kwallon kafar Najeriya (Dream Team) suka yi nasarar lashe babban zinarin Gasar Olympic da aka yi a Atlanta. Wannnan nasarar yana daya daga cikin gagarumin nasarar da kasar Najeriya tayi a tarihin wasan kwallon kafa wanda har yanzu mafi yawancin masoya kwallon kafan Najeriya ke alfahari da ‘yan wasan da suka nuna bajintar su a wannan lokacin. A yanzu kuna ganin tawagar kwallon kafar Najeriya zata iya kwatanta irin wannan bajintar a nan gaba kamar yanda na baya suka yi?…

Karanta...

Adamawa: An Shawarci Iyaye Da Tura ‘Ya’yan Su Makaranta

An kira yi iyaye da su kasance masu mai da hankali wajen tura ‘ya’yan su Makarantu domin kawo saukin yawaitar Yaran da basu zuwa makaranta a tsakanin yara baki daya. Shugaban Makarantar NAFAN ACADAMY Adamu Jingi wanda akafi sani da Maihange ne yayi wannan kira a lokacin bikin yayen daliban makarantar da ya gudana a harabar makarantar dake Jambutu a cikin karamar hukumar Yola ta arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa. Adamu yace baiwa yara ilimi abune da yake da matukan muhimmanci don haka bai kamata iyaye suyi sakaci da ‘ya’yan…

Karanta...

Kaduna: An Sace Malamin Jami’a

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna Yakubu Sabo, ya bayyana cewa masu garkuwa sun arce da wani malamin Jami’ar gwamnatin Tarayya dake Dutsinma, Katsina. Wanda aka yi garkuwa da, Abubakar Idris mazaunin unguwar Barnawa ne dake Kaduna. ” DPO na unguwar Barnawa ne ya sanar da mu abinda da ya faru cewa wasu da ba a san ko su waye ba sun tafi da Abubakar Idris a gidansa dake titin Lawal Ahmed, Barnawa Kaduna. ” DPO ya ce ko kafin su isa wurin masu garkuwan sun tafi da shi. Sai…

Karanta...