Yawaitar Kashe-Kashe: Mu Dage Da Addu’oi – Kiran Sheikh Bauchi Ga Sakkwatawa

Gwamnan jihar Sokoto Rt Hon Aminu Waziri Tambuwal CFR (Mutawallen Sokoto) tare da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Saad Aboubakar III, ya karbi bakuncin Shehin Malamin Addinin Islama Dahiru Usman Bauchi a gidan Gwamnatin Jahar Sokoto. Shehin Malamin yace, ya kawo wannan ziyarar ne domin jajantawa Maigirma Gwamna Tambuwal, Mai Alfarma Sarkin Musulmi tare da al’ummar Jahar Sokoto, akan Ibtila’in da ya faru a wasu daga cikin Kananan Hukumomin jahar Sokoto, inda ake zuwa ana kashe al’umma ba gaira ba dalili. Yayi fatar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukan su…

Karanta...

Bana Tsoron EFCC – Saraki

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa bai aikata wani laifin da a yanzu Hukumar EFCC ke kokarin tuhumar sa da su ba. Ya kuma kara da cewa shi bai shiga kafafen yada labarai ya na cacar-baki da EFCC ba. A cikin watan Mayu ne dai EFCC ta shafa wa wasu gideje jan fenti, tare da ikirarin cewa ta tabbatar Saraki ne ya saye su a hannun Kwamitin Sayar da Kadarorin Gwamnatin Tarayya da Shugaban Kasa ya kafa. EFCC ta ce Saraki ya sayi gidajen ne ta hannun…

Karanta...

An Bayyana Sabbin Shugabannin Majalisar Dattawa

Shugaban majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya bayyaana sabbin shugabannin majalisar dattawa. Ya karanta sunayen wadanda a ka nada ne a zauren majalisar dake kunshe cikin wasikun da shugabannin jam’iyyu suka mika masa. Wadanda aka nada sun hada da; Yahaya Abdullahi (APC, Kebbi) – Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar. Ajayi Borrofice (APC, Ondo) – Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye Orji Uzor Kalu – Mai tsawatarwa na Majalisa Aliyu Abdullahi (APC, Niger) – Mataimakin Mai tsawatarwa Enyinnaya Abaribe (PDP)- Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisa Emmanuel Bwacha (PDP, Taraba) – Mataimakin shugaban Marasa Rinjaye.…

Karanta...

Doguwa Ya Zama Sabon Shugaban Masu Rinjaye A Majalisar Tarayya

Jam’iyyar APC ta tsaida Alhassan Doguwa daga Jihar Kano matsayin Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Tarayya. Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole ne ya bayyana haka, a lokacin da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Nasiru Gawuna ya shugabanci tawagar da ta kai masa ziyasa a Abuja. Oshiomhole ya bayyana cewa “siyasa abu ne da ake tinkaho da yawan jama’a, ya ce APC ta zabi Doguwa, domin jihar Kano ce ta fi kowace jiha samar wa APC kuri’u a zaben shugaban kasa. “Don haka an ce alamun yaba kyauta shi ne a bayar…

Karanta...

Ban Karbi Sarautar Bichi Don Tozarta Sunusi Ba – Aminu Ado

Mai martaba Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero yace bai karbi sarautar Bichi da zummar cin mutunci ko ragewar sarautar Sarki Sunusi daraja ba. Sarkin ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai inda bayyana karbar sarautar ba a matsayin mataki na cin mutunci Muhammadu Sunusi II ba. Yace yakamata mutane su gane cewa komai yana iya chanzawa a kowana irin lokaci. “Tun cikin shekarar 1963 da mahaifina ya zama Sarkin Kano, abubuwa sukayi ta chanzawa, kuma zasu cigaba da chanzawa.” “Bari na baku wani misali; mahaifina ya nada…

Karanta...

Dalilin Da Ya Sa Na Maka Hadimar Buhari Kotu – Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya maka daya daga cikin hadiman Shugaba Muhammadu Buhari a kotu, inda ya nemi ta biya shi diyyar naira bilyan 2.5, domin ya sayi sabulun wanke kashin-kajin da ta goga masa, da sunan sa da ta bata a idon duniya. Atiku ya nemi kotu ta tilasta wa Lauretta Onochie ta ba shi hakuri dangane da labaran karairayi da kanzon-kurege wadanda ya ce Lauretta ta yi masa a shafin ta na Twitter da kuma Facebook. Lauretta dai ta na daya daga cikin hadiman Shugaba Muhammadu…

Karanta...

Kaduna: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Damke ‘Yan Ta’adda 62

Rundunar ‘yan sanda ta jiar Kaduna, ta ce ta kama akalla bata-gari 62 a cikin makwanni biyu. Kwamishinan ‘yan sandan Jihar, Mista Ali Janga ne ya bayyana hakan a wajen wani taron manema labarai da rundunar ta kira a hedikwatar ta da ke Kaduna. Kwamishinan ya ce, rundunar ta ci gaba da tsananta farautar ‘yan ta’adda da sauran masu aikata miyagun laifuka a baki-dayan jihar, sannan kuma tana ta ci gaba da tsara dubarun farmakan masu laifin da hanyoyin da suka hada da na rundunar, ‘Operation Puff Adder.’ Ya ce,…

Karanta...

Sama Da Kashi Goma Na ‘Yan Najeriya Mashaya Ne – Bincike

Likitan kwakwalwa kuma babban jami’i a asibitin masu tabin hankali na Maiduguri, babban birnin jihar Borno, Dr Ibrahim Abdullahi Wakawa, ya bayyana cewa a cikin shekarar da ta gabata a Najeriya an gudanar da wani bincike da ya nuna cewa kashi 14 cikin dari na al’ummar Najeriya su na ta’ammali da miyagun kwayoyin da ke gusher da hankalin mutane, wanda hakan na nufin a duk daya daga cikin ‘dan Najeriya shida za a iya samun mai amfani da kwaya. A jihar Borno kuwa binciken ya nuna cewa kusan 10 cikin…

Karanta...

Tsaro: Rundunar Soji Ta Nemi Taimakon ‘Yan Kasa

Rundunar sojojin Nijeriya ta bukaci ’yan Nijeriya su agaza ma ta a kokarin ta wajen tabbatar da dorewar zaman lafiya tare da kare ’yan kasa da dukiyoyinsu. Wannan kiran ya fito ne daga bakin babban hafsan sojojin Nijeriya, Laftanar-Janar Tukur Buratai, a taron zanta wa da manema labarai a Maiduguri, ranar Jumu’a da ta gabata, a shirye-shiryen gabatowar bikin tunawa da yan mazan jiya (NADCEL) da na makon baje karfin kwajin sojojin. Wanda a ke sa ran za a gudanar da wadannan bukukuwan a birnin Legas, tsakanin daya zuwa shuda…

Karanta...