Zaben Guinea: Buhari Ya Bada Tallafin Dala Dubu 500,000

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fitar da sanarwar cewa ya bai wa gwamnatin kasar Guinea Bissau dala 500,000, hade da kunshin kayayyakin aikin zabe guda 350, babura guda goma, motoci kirar Hilux guda biyar, da motar jigilar kayayyaki (a kori kura) guda biyu, a matsayin tallafi domin gudanar da zaben kasar. A dangane da sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da tallafin sakamakon kokon barar da kasar ta Guinea Bissau ta miko na a taimaka mata domin ta samu damar gudanar da…

Karanta...

Yahaya Bello Na Shirin Sayar Da Jihar Kogi – Melaye

A Juma’ar nan ne Sanatan al’ummar jihar Kogi ta tsakiya, Dino Melaye ya ce gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya kammala shirye-shiryen sa na siyar da jihar Kogi. Sanatan yayi wannan furuci ne yau a shafin sa na facebook, inda yace “jihar Kogi ta zama ta siyarwa, domin gwamna Yahaya Bello ya gama shirye-shiryen ciwowa al’ummar jihar Kogi bashin kudi Naira biliyan 32 daga bankin Sterling. “Idan bankin Sterling ya kuskura ya bada wannan bashin kudi, za mu garzaya kotu domin babu sauran wani yarda da kotu za tayi da…

Karanta...

Zamfara: Mata 8000 Sun Zama Zawarawa Yara 16000 Sun Zama Marayu – Yari

Gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari ya ce mata dubu 8,000 ne suka zama zawarawa, inda kuma yara dubu 16,000 suka zama marayu sakamakon ayyukan ‘yan ta’adda a jihar Zamfara. “Kididdigar da aka yi ya nuna cewa tun da aka fara ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane a jihar Zamfara, sama da mutane dubu 4,000 ne suka rasa rayukan su a jihar. “Inda kuma sama da mutane dubu 9,000 suka ji raunuka, kamar yadda gidaje da shaguna da rumbuna sama da dubu goma 10,000 aka lalata su. “Sama da al’umma dubu…

Karanta...

Rikicin Shi’a: Kwararrun Likitoci Daga Kasar Waje Sun Gana Da Ibrahim El-Zakzaky

A karon farko, gwamnatin tarayya ta amince ma wasu likitocin kasar waje samun ganawa da shugaban ‘yan shia Ibrahim Zakzaky domin duba lafiyar sa tun bayan kama shi a shekara ta 2015. Likitocin dai sun samu ganawa da El-Zakzaky ne bayan samun umarni daga Alkalin wata babbar kotu da ke Kaduna, wanda ke sauraren karar da gwamnatin jihar ta shigar da Malamin. Duba da halin rashin lafiya da El-Zakzakky ke ciki ne ya sa Alkalin ya umarci hukumar tsaro ta farin sirri su gaggauta gayyato masa likitocin da ya ke…

Karanta...

Neman Mata: Kungiyar Izala Ta Ja Kunnen Zababbun Gwamnoni Da ‘Yan Majalisu

Kungiyar Izalatil bidi’a Wa-Ikamatissunnah reshen jihar Filato, ta gargadi sabbin zababbun gwamnoni da ‘yan majalisun dokoki, game da neman matan da addini ya haramta masu bayan darewar su a kan karagar mulki. Shugaban majalisar Malamai ta kungiyar Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi wannan gargadi a wani taron kara wa juna sani da kungiyar ta shirya. Ya ce sun samu ingantattun bayanai bayan kaddamar da wani bincike a kan shugabannin siyasa, kuma sun gano cewa yawancin gwamnoni da ministoci da ‘yan majalisu da manyan jami’an gwamnati ba su yi aiki…

Karanta...

Magudin Jarabawa: Kwalejin Fasaha Da Kere-Kere Ta Nuhu Bamalli Ta Kori Dilibai 60

Hukumar makarantar Nuhu Bamalli da ke Zaria a jihar Kaduna, ta bayyana korar dalibai 60 saboda magudin jarabawa tun kakar karatun shekara ta 2017 da 2018. Rahotanni sun ruwaito cewa, an kori daliban ne a cikin zangon farko da na biyu na kakar karatun shekarun 2017 da kuma 2018. Shugaban makarantar Dakta Muhammad Kabir Abdullahi ya bayyana haka, a wajen bikin rantsar da sabbin dalibai dubu 5 da 813 na kakar karatun shekara ta 2018 da 2019. Dakta Muhammad Kabir, ya ce a cikin mutane dubu 15 da 114 da…

Karanta...

Rashin Albashi: Malaman Makarantun Sakandare Sun Yi Zanga-Zanga A Jihar Ekiti

Malaman makarantun sakandare a jihar Ekiti da tsohon gwamnan jihar Ayodele Fayose ya dauka aiki a shekarar da ta gabata, sun gudanar zanga-zanga biyo bayan rashin biyan su albashi na tsawon watanni bakwai. Rahotanni sun cem malaman sun roki gwamna Kayode Fayemi ya tausaya ya biya albashin da su ke bi bashi domin ya share masu hawaye. Daya daga cikin masu zanga-zangar Bayo Omoyemi, ya ce sun rubuta wasika zuwa ga gwamna Fayemi da matarsa da mataimakin gwamna da masu sarautun gargajiya, su na rokon da su ceci rayuwar su…

Karanta...

Tabarbarewar Tsaro: An Sace Wasu ‘Yan Kasar China Biyu A Jihar Ebonyi

Wasu masu garkuwa da mutane, sun sace wasu ‘yan kasar China guda biyu da su ka hada da wani  Sun Zhixin da Quing Hu da ke aiki a kamfanin gine-gine na Tongyi a jihar Ebonyi. An dai sace mutanen ne a daidai lokacin da su ke aikin hanyar karamar hukumar Ohaozara ta jihar Ebonyi, inda barayin su ka dauke su ta karfin tsiya su ka gudu da su. Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Odah Loveth ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce yanzu haka hukumar ‘yan sanda ta…

Karanta...

Matsalar Tsaro: ‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Sanda Uku Da Wani Mai Unguwa A Jihar Rivers

Wasu ‘yan bindiga sun kashe jami’an hukumar ‘yan sandan Nijeriya uku da wani mai unguwar Iriebe a karamar hukumar Oyigbo da ke jihar Rivers. Wata majiya ta ce ‘yan bindigar sun kai harin ne a ranar Larabar da ta gabata, inda su ka shiga garin da bindigogi da adduna su na yi wa al’ummar Hausawa da ke garin barazana. Jami’an tsaron yankin sun kai wa ‘yan bindigar hari, inda su ka samu nasarar kashe biyu daga cikin su. Sai dai a wani abu mai kama da daukar fansa, wasu daga…

Karanta...

Rufe Kasuwa: ‘Yan Kasuwar Gaidam Sun Koka Da Matakin Da Sojoji Su Ka Dauka

Kimanin makonni goma sha hudu kenan, tun bayan da rundunar Sojan kasa ta rufe wata babbar kasuwar hatsi da dabbobi da ke garin Gaidam ta jihar Yobe, inda ta ce hakan ya zama wajibi domin tabbatar murkushe ayyukan kungiyar Boko Haram. Sai dai ‘yan kasuwa da abokan cinikkayyar su sun koka, duba da tsawon lokacin da aka kwashe kasuwar ta na rufe, wanda hakan ya sa jama’a da dama sun shiga mawuyacin hali sakamakon kasuwar ta kwashe sama da shekaru 100 ta na aiki. Yawancin ‘yan kasuwar su na debo…

Karanta...

Ta’addanci: ‘Yan Fashi Sun Yi Garkuwa Da Jirgin Dakon Mai A Jihar Rivers

Hukumar kula da sufurin ruwa ta kasa da kasa, ta ce masu fashin teku sun kwace wani jirgin ruwa na dakon mai a Nijeriya, inda su ka sace matuka jirgin guda shida. Lamarin dai ya faru ne a kudancin birnin Fatakwal na jihar Rivers kamar yadda hukumar ta bayyana, inda ta ce tuni an sanar da rundunar sojan ruwa ta Nijeriya, kuma an kaddamar da bincike a kan lamarin. Idan dai za a iya tunawa, a farkon wannan watan, wasu masu fashin teku sun yi yunkurin sace wani jirgin dakon…

Karanta...

Rikicin Kaduna: An Sanya Dokar Hana Fita A Karamar Hukumar Kajuru

Gwamnatin jihar Kaduna, ta sanya dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24 a karamar hukumar Kajuru. Mai magana da yawun gwamnatin jihar Samuel Aruwan, ya ce hakan ya biyo bayan wata matsalar tsaro da ta faru a garin Kasuwar Magani. Aruwan ya ce an dauki matakin ne bayan wani zama da majalisar tsaro ta jihar Kaduna ta yi, ya na mai cewa an tura jami’an tsaro yankin kuma kura ta lafa. A cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta wallafa a shafin ta na Twitter, ta ce dokar ta fara…

Karanta...

Garambawul: Janar Buratai Ya Yi Wa Manyan Sojoji Sauyin Wuraren Aiki

Rundunar Sojin kasa ta Nijeriya, ta sanar da sabbin nade-naden mukamai ga wasu manyan hafsoshin soji a wani garambawul da Janar Tukur Yusuf Buratai ya ke gudanarwa a rundunar. Kakakin rundunar Kanal Sagir Musa ya bayyana sabbin nade-nade, inda ya ce Buratai ya amince a dauke Manjo Janar Sule Kazaure daga hukumar yi wa kasa hidima zuwa cibiyar tattara bayanai ta rundunar. An kuma nada Birgediya Janar S. Ibrahim a matsayin sabon shugaban hukumar NYSC, bayan ya dauke shi daga jami’ar rundunar sojin kasa da ke Biu a jihar Borno.…

Karanta...

Rikicin Kajuru: An Kashe Jami’an Soji Biyu Tare Da Raunata DPO

Wata majiya daga karamar hukumar kajuru ta jihar kaduna, ta tabbatar da cewa, an kashe jami’an soji biyu, tare da ji ma shugaban ‘yan sandan yakin ciwo, a wata arangama da akayi tsakanin jami’an tsaro da wasu ‘yan ta’adda. Majioyar, wadda ta bukaci a sakaya sunan ta, ta bayyana wa Liberty cewa, sojojin da lamarin ya rutsa da su, su na kokarin tabbatar da zaman lafiya ne a wasu yankuna da ke kajuru, inda ake yawan samun tashe-tashen hankula. Yanzu haka dai shugaban ‘yan sandan na yankin, wanda aka ji…

Karanta...

Tsaro: Shugaba Buhari Ya Bayyana Muhimmiyar Hanyar Yaki Da Ta’addanci

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana babbar hanya mafi inganci ta yaki da ayyukan kungiyar Boko Haram, inda ya ce samar da ingantaccen ilimi ne kadai hanyar kawar da Boko Haram daga Nijeriya. Buhari ya bayyana haka ne a birnin Maiduguri na jihar Borno, yayin da ya kaddamar da manya ayyukan more rayuwa da gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya yi. Shugaba Buhari ya tabbatar wa jama’ar jihar Borno cewa, ya na aiki tukuru don ganin ya ceto rayukan ‘yan matan Chibok da na Dapchi da kungiyar Boko Haram ta…

Karanta...