Mulkin Buhari Tamkar Rayuwa A Jahannama Ne – Jalade

Mashahuriyar ‘yar wasar finafinan nan ta Nollywood, Omotola Jalade Ekeinde, ta wallafa wani kira da ta yi ga Shugaba Buhari da Mataimakinsa Farfesa Osinbajo a shafinta na Twitter cewa: “Rayuwar Nijeriya a karkashin mulkin ku tamkar rayuwa ce a jahannama.” ‘Yar wasar ta kara da cewa: “Matsalar rashin kudi da matsalar kashe-kashen rayuka da ‘yan ta’adda ke yi zai sa kasar ta tarwatse. Rayuwa a Nijeriya aba ce mara yiwuwa!”

Karanta...

Ali Da Zango Nasiha Suke Bukata Ba Zuwa Kotu Ba

Ba zuwa kotu bane hanyar warware matsalar da take tsakanin Ali Nuhu Muhammad da Adam A Zango ba. Kotu ba zata iya warware matsalarsu ba din-din-din idan har basu ji tsoron Allah sun ajje hassada da hamayya ba. Gaskiya fa duk sanda mutane biyu suka hadu akan soyayyar abu guda daya sun zama maqiyan junansu kamar yadda Thomas Hobbes yace. Idan zamu duba maganar wannan masanin zamu gane cewa rikicin Kannywood ba zai ta6a sauki ba idan basu daina tseren mallakar sarautar kannywood ba. Ko wanne daga cikinsu baya so…

Karanta...

Rikicin Syria: Red Cross Ta Ce Ma’aikaciyar Na Raye

Kasar New Zealand ta tura runduna ta musanman domin ‘yanto wata jami’ar lafiya ta kasar Louisa Akavi, da mayakan IS suka yi garkuwa da ita a Syria tun a shekarar 2013. Wannan na zuwa ne bayan da kungiyar bayar da agaji ta kasa da kasa wato Red Cross da ta ke yi wa aiki ta ce ta samu wasu bayanai da ke tabbatar ma ta da cewa jami’an yar shekaru 62 na nan da ranta. An dai sace ma’aikaciyar lafiya tare da wasu direbobi biyu ‘yan Siriyan a yayin da…

Karanta...

Sudan: An Kama Jami’an Hambararriyar Gwamnatin Al Bashir

Gwamnatin mulkin soja ta Sudan ta damke jami’a hambararriyar gwamnatin Omar al-Bashir kuma sun yi alkawarin kyale masu zanga-zanga su ci gaba da boren da suke yi. Wani kakakin gwamnatin ya kuma ce an mika wa kungiyoyin da suke shirya boren da su nada wanda suke so ya zama firai ministan gwamnatin riko da za a kafa. Masu zanga-zangar dai sun sha alwashin ci gaba da nuna bacin ransu a bisa titunan biranen kasar har sai an mika mulki ga gwamnatin riko ta farar hula. Har zuwa yau masu boren…

Karanta...

Iftila’i: Gobara Ta Kone Shaguna 35 A Babbar Kasuwar Kano

Wata gobara ta kone shaguna akalla 35 bangaren ‘yan nama dake  kasuwar Kurmi a jihar  Kano. Mai magana da yawun hukumar kashe gobara a jihar Kano, Saidu Mohammed, ya bayyana haka a lokacin yake magana da manema labarai  a Kano. Ya ce da  misalin karfe 4:56 na safe ne,  wani mutum mai suna Ado Musa, ya kira sanar da hukumar cewar gobara ta tashi a kasuwar, amma  nan da nan jami’an hukumar kashe gobara, suka  isa wajen  da misalin karfe 5:03 domin hana wutar gobarar yaduwa zuwa sauran shaguna. Mohammed,…

Karanta...

Arewa Maso Gabas: Rundunar Sojin Najeriya Ta Kashe ‘Yan Boko Haram

Rudunar sojin Operation Lafiya Dole tare da hadin kan dakarun sojin kasar Chadi sun sami nasarar akan ‘yan kungiyar  Boko Haram a wata arangama da suka yi a arewacin jihar Borno. Kakakin sojin Najeriya, Kanal Sagir Musa, ya bayyana haka, inda ya ce  rundunar sojin sun hallaka yan Boko Haram 27 kuma sun kwato manyan makamai. Ya ce rundunar ta sami nasara ce a kauyukan Wulgo, Tumbuma, Chikun Gudu, da Bukar Maryam duk dai a jihar Borno. Kanal Sagir Musa, ya kara da cewar a lokacin  arangamar, an hallaka yan…

Karanta...

Bincike: ‘Yan Majalisa Sun Kashe Naira Biliyan 140 A Shekara Ta 2018

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya bada umarnin a bayyanawa Duniya abinda majalisar tarayya ta kashe a kasafin kudin shekara ta 2018. Kundin kasafin kudin majalisar da aka fitar mai shafi 45 ya nuna cewa ‘yan majalisar wakilai da kuma majalisar dattawa sun kashe kusan Naira Biliyan 140 daga kasafin kudi na  shekarar da  ta  gabata. Shugaban majalisar ya ce an warewa majalisa naira billiyan 139 da milliyan dari 5 a cikin kasafin shekara ta 2018, daga cikin kudin naira Biliyan 35 da millyan 5 sun  tafi wajen yan majalisar…

Karanta...

‘Yan Fashi Da Makami : Rundunar ‘Yan Sanda Ta Kashe Mutane ‘Yan Fashi 9 A Hanyar Abuja Zuwa Kaduna

Rundunar  ‘yan sandan Najeriya ta ce sami nasarar hallaka ‘yan fashi da makami 9 a dajin Akilbi kusa da  hanyar Abuja zuwa Kaduna. Mai magana da yawun rundunar DCP Frank Mba, ya ce hukumar ta yi galaba akan masu ta’ada ya yin wata misayar wuta a tsakanin su. Mba, ya ce hukumar ta sami nasarar cafke wasu miyagun makamai da suka hada da  bindigogi daban-daban tare da kwanson alburusai da kuma harsashai. Ya ce jami’in dan sanda guda ya raunata inda a halin yanzu ya ke jinya a asibiti. DCP…

Karanta...

Cire Tallafin Man Fetur: Kungiyar Kwadago Ta NLC Ta Ba Gwamnatin Tarayya Shawara

Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta ta ja kunnen gwamnatin tarayya ta guje daukar shawarar da Asusun bayar da lamuni na Duniya wato IMF ya bata na cire tallafin man fetur. Kungiyar ta ce idan gwamnati ta biyewa wannan shawara, za a sami karin farashin man fetur, wanda a karshen mutanen Najeriya za su shiga cikin wani mawuyacin hali. Shugaban kungiyar ta kasa Ayuba Wabba ya bayyana haka a  wajen wani taro na musamman da kungiyar kwadagon ta shirya a Abuja. Ayuba Wabba, ya  ce a duk lokacin da Asusun…

Karanta...

Yaki Da Rashawa: EFCC Ta Kwace Wasu Gidaje Mallakin Diezani Madueke

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Najeriya wato EFCC, ta yi nasarar karbe wasu kadarorin tsohuwar ministar man fetur Diezani Alison-Madueke. Ofishin hukumar EFCC dake jihar Legas ne ta sami nasarar karbe wasu dukiyoyi na Diezani Alison da kuma wani mutum mai suna Donald Chidi Amangbo. Daga cikin kadarorin da hukumar ta sa aka karbe akwai wani makeken gida dake titin Nnmadi Azikiwe a Fatakwal na jihar Ribas. Mai shari’a na babbar kotun tarayya da ke Legas Chuka Obiozor ya bada damar karbe wadannan…

Karanta...

Tsaro: Kungiyar SERAP Ta Nemi Wasu Bayanai

Kungiyar mai yaki da rashawa da kuma  tabbatar da shugabanci na gari  wato SERAP, ta nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni 36, su yi wa kasa bayanin abubuwan da su ke yi da kudaden da ake warewa domin inganta tsaro. Kungiyar ta nemi bayanin kudaden tsaron, ciki har da wani bangare da aka fi sani da Security Vote, a wata takarda ta musamman da ta aike wa shugaban kasa da gwamnonin sa. Takardar wacce ke dauke da sa hannun mataimakin shugaban kungiyar, Kolawale Oluwadare, ta ce sashi na 14,…

Karanta...

Hukumar FRSC Ta Gargadi Jami’an Ta Su Daina Bin Masu Laifi A Guje

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa ta gargadi jami’an ta su daina bin masu laifi a guje ko da kuwa sun aikata laifi. Jami’i mai kula da sashen wayar da kan jama’a na hukumar Bisi Kazeem ya bada wannan sanarwa, yayin da ya zanta da manema labarai a Lagos. Kazeem ya bayyana haka ne, a daidai lokacin da ya ke jawabi akan hadarin da ya auku ranar Juma’a a garin Ibadan sakamakon bin masu laifin da jami’an hukumar su kayi. Ya ce hakika Shugaban hukumar ya nuna bacin ran sa bisa…

Karanta...

Lauyan Atiku Ba Ya Da Lasisin Shiga Harkokin Shari’a A Najeriya – INEC

Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta ce korafin da Atiku Abubakar ya gabatar a gaban kotun bai samu sa hannun Lauya mai lasisin shiga harkokin shari’a a Nijeriya ba. Atiku Abubakar dai ya shigar da korafi a gaban kotun daukaka kara, domin kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu na shekara ta 2019. Yanzu haka dai kimanin lauyoyi 32 ke wakiltar Atiku Abubakar a kotu, a karkashin jagorancin babban Lauya Livy Uzoukwu. Sai dai hukumar zabe ta ce, Lauyan…

Karanta...

Albashi: Kungiyar Kwadago Ta Ba Shugaba Buhari Nan Da 1 Ga Mayu Ya Sa Hannu

Kungiyar kwadago ta kasa NLC, ta ba shugaba Muhammadu Buhari wa’adin nan da zuwa ranar 1 ga watan Mayu ya sa hannu kan sabuwar dokar karin mafi karancin albashi daga Naira 18,000 zuwa Naira 30,000. Shugaban kungiyar na kasa Kwamred Ayuba Wabba ya bayyana haka, yayin wata zantawa da ya yi da manema labarai a Abuja. Ya kuma yi tsokaci akan ikirari da gwamnatin tarayya ta yi na kara farashin man fetur, ya na mai cewa tun a tashin farko, da dama ba su san ma akwai wani wai tallafin…

Karanta...

DCP Abba Kyari Ya Cafke Wasu Manyan Masu Satar Mutane A Imo

Wasu masu garkuwa da mutane su bakwai da aka kama kwanan nan, sun bayyana yadda su ka kashe wani Ba’Amurke a cikin jihar Imo a shekara ta 2017. ‘Yan ta’addan dai sun shiga hannun babban jami’in dan Sanda DCP Abba Kyari da ‘Yan Tawagar sa na musamman. Wadanda aka kama kuwa sun hada wani Sunday Igwe, da Michael Ahmefula, da Oyebuchi Echefule, da Ndubusi Isaac, Victor Dagogo, da Chima Okoro da kuma John Edet. ‘Yan ta’addan dai sun tabbatar da cewa, su ne ke yin fashi da makami, kuma su…

Karanta...