Magudi Aka Yi A Kano Ba Zabe Ba- Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Kano,Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya wallafa rubutu a shafinsa na facebook cewa ba a yin zabe a jihar Kano gaba daya sai murdiya kawai ake yi yanzu haka. Sannan ya yi sharing link yake cewa Mataimakin babban Sufeta Janar na ‘yan sandan Nijeriya DIG Anthony Ogbizi Michael da aka turo Kano ya zo ya karbi ragamar umarni da tabbatar da tsaro ya wargaza dukkan tsarin da aka yi na tabbatar da tsaro. A gefe daya kuma, Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kano Rabiu Sulaiman Bichi ya bayyana ya…

Karanta...

Zaben Kano: Baza Mu Taba Amincewa Da Wannan Karfa Karfan Ba – PDP

Jam’iyyar PDP a Jihar Kano, ta ki amincewa da zaben da ake ci gaba da gudanarwa yau a jihar Kano. Ana gudanar da zaben ne a wasu rumfunan zabe a Kananan Hukumomi 28 daga cikin 44 na fadin jihar. Shugaban Jam’iyyar PDP, Rabi’u Bichi ne ya bayyana haka da ya ke yi wa manema labarai jawabi a Kano. Ya ce PDP ba ta amince da zaben ba, saboda ya zo da hargitsi tare da kai wa magoya bayan PDP hari, hana su yin zabe da kuma ji wa da daman…

Karanta...

Gayyata: Macron Ba Zai Halarci Taron Juyayin Kisan Kiyashin Rwanda Ba

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ba zai halarci taruruka da addu’o’in cika sekaru 25 da barkewar kisan kiyashin kasar Rwanda da za a yi ranar 7 ga watan afrilu mai zuwa ba. Sakamakon kusancin da aka samu tsakanin Faransa da Rwanda bayan hawan Macron karagar mulki, wannan ya sa gwamnatin Rwanda aike wa shugaban da goron gayyata domin ya halarci wadannan adu’o’i da za a yi a birnin Kigali, to sai Macron, ya ce zai tura wani dan majalisar dokokin kasar mai suna Herve Berville, domin ya wakilce shi. Herve Berville,…

Karanta...

Hadarin Mota: Mutane 60 Sun Mutu A Ghana

Akalla mutane 60 ne suka rasa rayukan su sakamakon hadarin da wasu motocin daukar fasinja biyu suka yi a yankin Bono da ke kudu maso gabashin kasar Ghana. Mai magana da yawun ‘yan sandan kasar ta Ghana Joseph Antwi Gyawu, ya ce motocin sun yi taho mu-gama ne da misalin karfe biyu na daren. Bayanai sun ce bayan da motocin suka yi taho mu-gama, nan take daya daga cikin su ta kama da wuta, bayan kowace mota na dauke da fasinjoji  50 a cikin ta. Kwame Arhin, likita a asibitin…

Karanta...

Hargitsa Zabe: An Cafke Kwamishinan Ganduje

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke kwamishinan Ayyuka na musamman na jihar Kano, Mukhtar Yakasai. ‘Yan sandan sun kama yakasai ne a daidai ya na kokarin tarwatsa zabe a rumfunar zabe da ke karamar Hukumar Dala. Tare da Yakasai akwai wasu gungun yan taratsi da ya jagoranta zuwa wadannan mazabu, duk an tarkata su zuwa caji ofis.

Karanta...

Kasuwanci: Noman Kayan Miya Na Taimakon Tattalin Arzikin Najeriya

Shugaban kungiyar sayar da kayan miya wanda yake kula da kasuwancin bangaren tattasai a babbar kasuwar sayar da kayan gwari wadda take cikin unguwar Mile 12 a jihar Legas Dauda Suleman Tarai, ya bayyana cewa noman kayan miya da manoman Arewa ke yi yana taimaka wa Najeriya da al’ummar cikin ta baki daya. Dauda Sulaiman, ya yi wannan bayani ne a offishin sa da ke Mile 12 a lokacin da yake zantawa da wasu manyam manoman kayan miya daga Arewacin Nijeriya da suke kawowa Legas domin sayar wa al’umma. Ya…

Karanta...

Trader Moni: Fadar Shugaban Kasa Ta Ce Har Yanzu Shirin Na Gudana Kamar Yadda Aka Tsara

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa rade-radin da ake yi na cewa gwamnatin tarayya ta tsaida shirin Trader Moni ba gaskiya bane. Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yayi wannan bayani ta bakin babban Hadimin sa. A wani jawabi da Laolu Akande ya fitar a madadin ofishin mataimakin shugaban kasar, yace har gobe Trader Moni na aiki kuma an samu kananan ‘yan kasuwa har 30, 000 da aka rabawa jari bayan an kammala zaben Najeriya. A wani jawabi da Laolu Akande ya fitar a madadin ofishin mataimakin shugaban kasar, yace har…

Karanta...

Martani: INEC Ta Tabbatarwa Amurka Cewa Ba Kasar Da Ba A Samun Korafe-Korafen Zabe

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ta mayar da martani a kan sanarwar da kasar Amurka ta fitar game da babban zaben 2019 da aka gudanar a Najeriya. Amurka ta ce bata ji dadin yadda yawancin al’umma ba su fito zaben ba tare da amfani fiye da sojoji fiye da kima a yayin gudanar da zabukan.Wani sashi na cikin sakon da Amurka ta fitar ya ce: A matsayin mu na tsaffin abokan huldar Najeriya, za mu cigaba sanya idanu a kan zaben da ake gudanarwa. Ba mu da wata jam’iyyar…

Karanta...

Kula Da Lafiya: Sama Da Mutane Miliyan 3 Ke Bukatar Ruwan Sha A N-Jeriya – UN

Asusun kula da kananan yara na duniya UNICEF ya ce  sama da mutane miliyan uku da rabi ne  ke bukatar tsabtacaccen ruwa a Nijeriya.   Asusun ya kara da cewa, wani jami’in ta da ke Nijeriya Muhammed Fall ya bayyana hakan a ranar juma’ar da ta gabata, a lokacin wani taron murnar ranar ruwa ta dunya.   Muhammad Fall ya kara da cewa, mutane sama da miliyan daya wadanda rikice-rikice ya raba su da gidajen su, wadanda da yawa daga cikin su suna fama da wannan matsalar ta rashin tsabtacaccen…

Karanta...

Kudin Makamai: Jami’an Tsaro Sun Kama Raymond Dokpesi Bisa Zargin Almundahana

Jami’an tsaro sun kama shugaban kamfanin yada labarai na AIT Raymond Dokpesi a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, jim kadan bayan dawowar sa daga kasar Dubai domin duba lafiyar sa.   Kamfanin gidan Talabijin na AIT ne ya sanar da haka, inda ya ce daya daga cikin jami’an hukumar hana shige da fice ta kasa ya ce, umurni ne suka samu daga sama na cewa su kama shi da zarar ya dawo Nijeriya.   Idan dai ba a manta ba, Raymond Dokpesi dai…

Karanta...

Sake Zabe: APC Da PDP Na Ribibin Lashe Kujeru A Zaben Gwamna

Kotun sauraren korarraikin zabe da ke birnin Abuja ta ayyana dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP, Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben jihar Osun bayan ta soke nasarar da Adegboyega Oyetola, na jam’iyyar APC ya samu a zaben da aka gudanar a watan Satumban 2018. Tuni kotun ta umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, ta Najeriya INEC ta mika sabuwar takardar nasara ga Adeleke. Wannan na zuwa ne bayan karar da Adeleke, ya shigar a gaban kotun, yana mai kalubalantar sakamakon da INEC ta fitar tare da zargin…

Karanta...

Sake Zabe: APC Da PDP Na Ribibin Lashe Kujeru A Zaben Gwamna

A yau ne hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ke gudanar da karashen zaben Gwamna a mazabun wasu jihohi, in da gwamnonin da ke kan karaga ke fafatawa da abokan hamayyar su da ke neman kawar da su daga madafun iko. Jihohin da ake gudanar da karashen zaben sun hada da Kano, da Sokoto, da Filato, da Benue, da kuma Bauchi,  bayan Hukumar ta INEC ta bayyana zaben jihohin a matsayin wadanda ba su kammala ba tun a ranar 9 ga wannan wata na Maris. Kodayake INEC ta…

Karanta...

Ko Sau Goma Akayi Zabe a Kaduna Atiku Ba Zai Yi Nasara a Kaduna Ba – El-Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana wa manema labarai a fadar shugaban kasa cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar mafarki ya ke yi cewa da yayi wai shine ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Kaduna. ” Atiku bai taba yin nasara a zaben shugaban kasa a Kaduna ba. Tun da shugaba Muhammadu Buhari ya fara takara a 2003, zuwa 2015 PDP bata taba yin nasara a zaben shugaban kasa a jihar Kaduna ba. Saboda haka ba yanzu bane za a ce wai Atiku yayi…

Karanta...