2023: Mika Ragamar Mulki Hannun Inyamurai Ne Mafita – Austin Braimoh

Labarin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar yayin da aka fara yakin neman zaben 2023, shahararren ‘dan gwagwarmayar nan, Austin Braimoh ya ba jigon APC, Asiwaju Bola Tinubu shawara akan makomar babban zaɓe dake tafe.

Austin Braimoh yana cewa ya kamata Asiwaju Bola Tinubu ya hakura da burin zama shugaban Najeriya, ya ba ‘Yan Ibo dama, suma jarraba tasu sa’ar a gani.

Da yake magana da ‘yan jarida a ranar Laraba, 8 ga watan Disamba, 2021 a birnin tarayya Abuja, Braimoh ya yi kira ga manyan jam’iyyun siyasa su kai tikitinsu zuwa kudu maso gabas.

Mista Austin Braimoh yana ganin adalci da neman zaman lafiya shi ne jam’iyyun siyasa su mika tutar takarar shugaban kasar su ga wanda ya fito daga yankin Ibo. “Arewa a dunkule ta ke shiyasa yanki daya zai iya fito da shugabannin kasa a jere, kuma ba za ayi wani rikici ba, amma babu irin wannan a Kudu.”

“Ina kira ayi watsi da ‘yan siyasan da suke bada shawarar ayi watsi da tsarin kama-kama, a daina la’akari da su a wajen neman mukami.”

Braimoh yace masu wannan ra’ayi ba su da adacli, kuma ba za samu zaman lafiya a haka ba. “Ina kira ga jagoranmu, ubanmu, Bola Tinubu, na san ya na da hakuri, na san idan lokaci ya yi, zai fito yace ya janye takara, ya goyi bayan Ibo.”

Labarai Makamanta