Ƙetare: Sojoji Sun Kifar Da Gwamnatin Kasar Myanmar

Sojojin Kasar Myanmar ko Burma suka kifar da gwamnatin Aung San Suu Kyi shugaban kasar Myanmar wacce ta ke yiwa ‘yan uwa Musulmi ‘yan kabilar Rohingya kisan kare dangi

Bayan sojojin kasar sun mata juyin mulki saboda rikicin siyasa, yanzu haka sun kamata tare da wasu manyan mukarrabanta sun tsare, rundinar sojin kasar ta sanya dokar ta baci a duk fadin kasar

Sojojin Myanmar sun mika shugabancin Kasar wa babban kwamandan sojojin Kasar General Min Aung Hlaing, sannan sojoji sun mamaye titunan manyan biranen Kasar

Alhamdulillah
Alhakkin ‘yan uwa Musulmin Rohingya ya kama ‘yar ta’adda Aung San Suu Kyi, Allah Ya kawo wa Musulmi agaji daga hannun ‘yan uwanta, abinda ya rage shine a mikata zuwa kotun duniya don ta fuskanci hukuncin kisan kare dangi, cin zarafi da take hakkin bil’adama

Yaa Allah Ka hada Aung San Suu Kyi da mummunan karshe Amin

Labarai Makamanta

Leave a Reply