Ƙetare: An Yi Yunƙurin Juyin Mulki A Nijar

A cikin daren Talata wayewar yau Laraba, da Misalin Karfe 3 ne aka jiyo harbe- harbe a fadar gwamnatin kasar jamhuriyar Nijar da ke a babban birnin Yamai.

Rahotanni sun nuna cewa an kwashe sama da mintoci 15 ana jin harbe-harben kafin daga bisani abin ya lafa.

Ya zuwa yanzu dai babu wani cikakkyen karin bayani akan abin da ya wakana. Amma rahotannin sun nuna cewa kura ta lafa komai na tafiya dai dai kamar yadda aka saba.

Masu sharhi kan lamurran yau da kullum na ganin daga irin wadannan harbe-harbe ne ake yunkurin juyin mulki.

A ranar Juma’ar nan 2 ga wata ne za a rantsar da sabon shugaban kasar ta Nijar Bazoum Mohammed bayan ayyana shi da hukumar zabe da Kuma kotun tsarin mulki na kasar suka yi a matsayin wanda ya lashe zaben Shugabancin kasar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply