Ɓatar Kuɗin Makamai: ‘Yan Jarida Sun Juya Mini Kalamai – Mungono

Mai ba Shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro Janar Mungono ya fito ya yi karin haske a kan kalaman da ya yi a game da salwantar kudin makamai.

A wani jawabi da ya fitar, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya) ya ce ‘yan jarida sun rikada kalamansa bayan hirar da ya yi da BBC Hausa.

Babagana Monguno ya bayyana cewar a hirar da aka yi da shi, babu inda ya nuna an yi awon-gaba da kudin makamai.

A cewarsa, ya jaddada kokarin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ne na maganin rashin tsaro ta hanyar ba jami’an sojoji duk kayan aikin da suke bukata.

“Hankalin Mungono ya zo ga wasu rahotanni da gidajen jaridu su ke yi daga wata hira da aka yi da sashen Hausa na BBC.” “Mu na so mu bayyana cewa an juya abin da mai bada shawara a harkar tsaron ya fada, domin babu inda ya fito bar-baro ya ce kudin makamai sun bace a karkashin tsofaffin hafsoshin tsaro.”

“A hirar, Mungono ya shaida wa ‘dan jaridar BBC Hausa, shugaban kasa ya ware makudan kudi da nufin a sayo makamai, amma kayan ba su isa ba, ko ba su karaso ba.” Jawabin ya ce Janar Babagana Monguno bai nuna wadannan kudi sun bace a lokacin da tsofaffin shugabannin tsaro su ke ofis ba, kamar yadda wasu su ka yaɗawa.

Janar Babagana Monguno ya kuma sanar da ‘dan jarida Mai girma shugaban kasa ya na bin kadin kwangilar fansar kayan yaki.” Ya ce a kan iya samun canjin lokacin isowar kaya.

Duk masu wasu tambaya a kan sayen makamai sai su tuntubi ma’aikatar tsaro, jawabin ya ce jami’an tsaro na kokarin shawo kan matsalolin da ake fama da su.

Labarai Makamanta