Kungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN) ta mayar da martani ga hukuncin kisa da aka yanke wa wani matashi mai suna Yahaya Aminu Sharif wanda ya yi batanci ga Manzon Allah SAW a Kano.
Idan za a iya tunawa, kotun Shari’ar Musulunci da ke Kano ta yanke hukunci kisa ga wanda ya yi batanci Manzon Allah.
Da yake tsokaci game da faruwar lamarin wanda ya haifar da ce-ce-kuce ga jama’a, Adeolu Samuel Adeyemo shugaban kungiyar CAN ta jihar Kano ya ce kungiyar ba ta da hujja tunda hukuncin ya yi daidai a tsarin musulunci.
Ya ce “a gare mu a cikin CAN hukuncin kotun shari’ar musulunci yana da mihammanci don haka kuma ba mu da wata hujja da za mu soki hukuncin.
Adeyemo yace a cikin Kiristanci batanci ga Ruhu Mai Tsarki ba za a gafartawa wanda ya aikata haka ba.
Ya kara da cewa kutse a cikin hukuncin Musulunci bai dace ba ga duk wani kirista.
You must log in to post a comment.