Ƙyamatar Rashawa Ya Sanya Ni Jefar Da Aiki Da Hukumar NDDC – Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Rabiu Kwankwaso, ya bayyana cewa shi ya ki jinin cin hanci da rashawa a rayuwarsa.

Kwankwaso ya fadi haka a hira da ya yi da BBC Hausa yana mai cewa sun yi hannun riga da cin hanci da rashawa.

“Cin hanci da rashawa ne ya durkusar da kasar nan. Za ka ga mutum a gwamnati yana satar kudi don azurta kansa amma maimakon aa hukuntashi, karshenta ma za ku gan shi a can sama ana damawa da shi a Harkokin gwamnati.

Daga nan sai ya yi tsokaci game da yadda cin hanci da rashawa, satar kudin al’umma da ya kanannade hukumar NDDC.

” Da kaina na hakura da ci gaba da zama kwamishina a hukumar NDDC a 2010 saboda mahaukacin satan kudin gwamnati da ake yi a hukumar. Da naga ba zan iya ba na tattara nawa inawa na hakura da hukumar.

Sai dai kuma idan ba a manta ba, shi kansa Kwankwaso ya taba fadawa tarkon hukumar EFCC bayan an Kai mata korafin ya waske da kudin kananan hukumomi har naira Biliyan 3.4.

An zargeshi tilasta wa kananan hukumomin su zaro kudadensu su yi masa kamfen din shugaban kasa a wancan lokaci, Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Idan ba a manta ba hukumar NDDC ta fada Cikin kallin yan majalisar kasa, inda take bincikar shugabannin hukumar da zargin yin watanda da kudaden hukumar a tsakaninsu Babu kakkautawa.

A cikin binciken da aka yi an gano har rabawa juna suke yi kudade babu kakkautawa, wai da sunan tallafin corona, su ma su ji sanyi-sanyi.

Labarai Makamanta