Ƙungiyar Matasan Arewa Ta Gargaɗi ‘Yan Arewa Kan Tafiye-Tafiye Zuwa Kudu

Kungiyar matasan Arewa ta NYCN ta nuna damuwa kan kashe-kashen ‘yan Arewa da ake yi, musamman a Kasuwar Shasha dake karamar hukumar Akiyele ta jihar Oyo.

Sun baiwa ‘yan Arewa shawarar cewa su dakata da tafiye-tafiye zuwa kudu saboda matsalar tsaron da ake fuskanta.

Kakakin kungiyar, Mock Kure ya bayyana cewa, suna Allah wadai da lamarin kuma suna kira jami’an tsaro su dauki matakin kawo karshen lamarin da hukunta wanda aka samu da laifi.

Labarai Makamanta