Ƙetare: Yariman Saudiyya Ya Gana Da Ɗan Marigayi Idriss Deby


Yariman Saudiyya mai jiran gado Mohammed bin Salman bin Abdulaziz da mataimakin Firaminista da kuma ministan tsaro sun tattauna da shugaban sojin Chadi Mahamat Idriss Deby. Ta wayar tarho a ranar Lahadi.

Kamfanin dillacin labaran Saudiyya SPA ya ce Yarima bin Salman ya yi wa Janar Mahamat Deby ta’aziyyar rasuwar mahaifinsa Idriss Deby wanda ya rasu a ranar Litinin sakamakon samun raunuka a fagen daga.

Yariman ya yi wa Chadi fatan ɗorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

A nasa ɓangaren kuma Janar Mahamat ya gode wa Yariman kan karamcin da ya nuna masa.

Labarai Makamanta