Ƙarin Kuɗin Makaranta: Ɗaliban Jami’ar Kaduna Sun Yi Zanga-Zanga

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Daliban Jami’ar Jihar Kaduna, KASU, a ranar Talata sun tare babban titin zuwa gidan gwamnati a Kaduna, babban birnin jihar don yin zanga-zanga kan karin kudin makaranta da gwamnatin jihar ta yi wanda ya wuce tunanin mai tunani.

Jami’ar mallakar gwamnatin jihar ta sanar da karin kudin makaranta da kimanin 600% daga N26,000 da aka saba biya a baya, lamarin da ya haifar da ruɗani a fadin Jihar.

A cewar sabon tsarin kudin makarantar da aka gabatar, ‘yan jihar za su rika biyan N150,000 yayin da abokan karatunsu a bangaren likitanci da kimiyya za su rika biyan N170,000 zuwa sama duk shekara.

A kan hakan ne daliban suka fito yin zanga-zanga suka rufe manyan titunan da za su bulla zuwa gidan gwamnati dauke da takardu masu sakonni daban-daban na nuna kin amincewarsu da karin wanda suka bayyana shi a matsayin na rashin imani.

Wannan zanga-zangar da daliban suka yi ya janyo cinkoson ababen hawa a wasu sassan jihar suna mai cewa dole gwamnatin jihar ta saurari kokensu ta biya musu bukatunsu.

Wasu daga cikin daliban sunyi addu’o’i a kan babban titin yayin da wasu daga cikinsu ke kula musu da titin. Jami’an tsaro suma sun hallarci wurin zanga-zangar domin tabbatar da ana bin doka da oda.

Daliban sun koka da cewa karin da aka yi zai saka wasu da dama cikinsu su daina karatun domin ba za su iya biya ba.

Don haka suke kira ga gwamnatin jihar ta janye karin kudin makarantar. Sunyi kira ga Gwamna El-Rufai wanda ya ce cikin tsarinsa zai tabbatar yaran talakawa sunyi karatu ya saka baki cikin lamarin. Jami’ar na da dalibai kimanin 19,000 cikinsu 17,000 yan asalin jihar ne.

Labarai Makamanta